• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUSULMI SUN KARA TAKARKAREWA GA AMFANA DA SAURAN RANAKUN RAMADAN NA HIJIRA 1442

ByYusuf Yau

May 9, 2021 ,

Al’ummar musulmi sun kara takarkarewa ga ibada don amfana da sauran ranakun da su ka rage na watan Ramadana na bana hijira 1442.

A Abuja a kan ji sautin sallah a masallatai a anguwanni daban-daban musamman da dare wajen dogayen sallolin nafila.

Kazalika mutane kan yi amfani da akalla sayen kwanon dabino ne su rika rabawa sauran jama’a daidai lokacin buda baki.

Har dai zuwa bana akwai masallatan da ba sa daukar nauyin masu itikafi don batun yaki da cutar annoba ta korona.

A duk shekara, lokacin Ramadan kan zama damar yin tafsiri da yawaita aiyukan alheri da yi wa kasa addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *