• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUNA SON A TURA ROTIMI AMEACHI GIDAN YARI DON ZARGIN SABA KA’IDA

Wani kamfanin Najeriya “INSIGHT DYNAMIC RESOURCES” ya shigar da kara babbar kotun taraiya ta Abuja ya na bukatar ta tura ministan sufuri Rotimi da shugaban hukumar fidda kwangila BPP Mamman Amadu gidan yari don zargin saba ka’idar ba da kwangilar shunfuda titin dogo da zai lashe dala biliyan 3.2.

Kamfanin INSIGHT ta hannun wanda ya jagoranci shigar da karar Musa Ibrahim Kuchi ya ce an yaudari majalisar zartarwa ta nuna cewa kamfanin SIN CCECC ne kadai a ka tura sunan sa don ba da kwangilar, alhali tun farko bankin EXIM na Amurka da kamfanin AECOM na Amurka sun mika takardun neman kwangilar.

Kuchi ya yi zargin tura sunan kamfanin Sin na nuna neman zarmiya ne don kamfanin AECOM da ya nemi aikin tun 2018 ya bukaci a gudanar da lamarin tsakanin gwamnatin Najeriya da Amurka ne da hakan zai toshe kafar samun na-goro a aikin.

Cikin wadanda a ka nema don amsa karar har da gwamnatin Najeriya da samun wakilicin ministan shari’a Abubakar Malami.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MUNA SON A TURA ROTIMI AMEACHI GIDAN YARI DON ZARGIN SABA KA’IDA”
  1. After looking into a number of the blog posts on your site, I
    honestly like your technique of writing a blog.
    I saved as a favorite it to my bookmark website list and will be checking back in the
    near future. Take a look at my web site too and tell me what you think.

Leave a Reply

Your email address will not be published.