• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUN ZABI JEFA BOMA-BOMAI KAN ‘YAN TA’ADDA DA BATUN BIYAN FANSA-ELRUFAI

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru Elrufai ya ce gwamnatin sa ta zabi jefa boma-bomai kan masu satar mutane maimakon bugewa da ba da kudin fansa da hakan tamkar karawa barayin karfi ne.

Kamar yanda jaridar Premium Times ta ruwaito daga wani faifan bidiyo da ta samu, gwamnan ya ce sun shirya da jami’an tsaro don dirar mikiya da boma-bomai kan barayin da hakan zai iya kai ga asarar wasu daga daliban da a ka sace amma za a samu nasarar hallaka dukkan ‘yan miyagun.

Gwamnan ya nuna an kammala shirin gudanar da farmakin sai kwatsam barayin su ka sullube daga da’irar da jami’an tsaro su ka zagaye su har hakan ya kai ga sako daliban kolejin kimiyyar gandun daji na Afaka.

Har yanzu dai gwamna Elrufai na kan bakan sa na kin ba da kudin fansa ga barayin don hakan karfi ne ga barayin da zai kara ba su damar sayo makamai da cigaba da sace mutane.

Duk da haka bayanai na tabbatar da iyayen wadanda a ka sace ko ‘yan uwan su kan tara kudi da ba da fansa don ceto ‘yan uwan su da a ka sace.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MUN ZABI JEFA BOMA-BOMAI KAN ‘YAN TA’ADDA DA BATUN BIYAN FANSA-ELRUFAI”
  1. After checking out a handful of the blog articles on your web site, I
    honestly appreciate your technique of writing a blog.
    I added it to my bookmark webpage list and
    will be checking back soon. Please check out my
    website too and let me know your opinion.

Leave a Reply

Your email address will not be published.