• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUN SAN ABUN DA YA KE FARUWA A KADUNA-GWAMNATIN NAJERIYA

Gwamnatin Najeriya ta ce ta na sane da abun da ya ke faruwa na takaddama tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin jihar Kaduna.

Ministan kwadago na Najeriya Chris Ngige ya ce gwamnatin taraiya na sane don haka ya na kira ga sassan biyu su maida wukake don samun sulhu.

‘Yan kwadagon dai na nan a cikin Kaduna karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Ayuba Wabba da zummar matsawa gwamnatin lamba ta janye shirin ta na korar dubban ma’aikata daga aiki.

A nan ta gefe gwamnatin ta Kaduna ta Nasiru Elrufai ta dage cewa ba za ta fasa korar ma’aikatan ba don su ke lashe fiye da kashi 90% na kudin shigar jihar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *