• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUN MARA BAYA GA ZABEN KASHIM SHETIMA A MATSAYIN MATAIMAKIN TINUBU-GWAMNONIN APC

ByNoblen

Jul 13, 2022

Kungiyar gwamnonin APC ta mara baya ga zaban Kashima Shetima a matsayin mataimakin Bola Tinubu a zaben 2023.

Shugaban kungiyar gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya zaiyana haka a lokacin da ya gana da shugaba Buhari a Daura.

Wannan dai na nuna gwamnonin sun mika wuya ga zaben Shetima maimakon daukar daya daga cikin su ya zama mataimakin.

Tun farko an yayata cewa gwamnan Kaduna Nasiru Elrufai da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na daga cikin wadanda a ke sa ran ba wa mukamin.

Hakanan shi ma gwamnan jihar Borno Umara Zulum ya nuna farin ciki da cankar Shetima a mataimakin, duk shi an yi ta yayata sunan sa don daukar sa a mukamin.

Zulum ya zaiyana wannan abun tamkar shi a ka yi wa don Kashim maigidansa ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MUN MARA BAYA GA ZABEN KASHIM SHETIMA A MATSAYIN MATAIMAKIN TINUBU-GWAMNONIN APC”

Leave a Reply

Your email address will not be published.