• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUN KIRGA MUTUM 52 DA ‘YAN BINDIGA SU KA KASHE A KAUYUKAN ANKA-MURTALA WARAMU

Daya daga mazauna kauyukan karamar hukumar Anka a jihar Zamfara, Murtala Waramu ya ce shi da sauran jama’a sun kirga gawa 52 da ‘yan bindiga su ka yi wa kisan gilla a wani mummunan farmaki da su ka kawo.
Murtala wanda yak e cikin masu gudun hijira a Anka ya ce har yanzu sun a ta binciken sauran mutane da ba a gani ba don sanin ko su na raye ko kuwa a’a.
Murtala ya ce da sun samu kwarin guiwa daga jami’an tsaro, za su iya fatattakar barayin da amfani da bindigar su ta harbi-ka-ruga.
A yanzu dai a cewar Murtala, mutane sun samu an bude mu su makarantun firamare a garin Anka inda su ke samun mafaka.
Da alamun kurar harin ta lafa don ‘yan bindigar sun wuce da kungurmin daji bayan sace dabbobin gida da jama’ar kauyukan ke kiwo.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *