• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUN KAMA HANYAR LASHE ZABEN 2023-SAKATAREN PDP

Babban sakataren jam’iyyar PDP na kasa Sanata Umar Tsauri ya ce jam’iyyar ta Kama hanyar lashe zaben 2023 don yanda APC ta yi wa adawa kamfen ta gazawa wajen cika alkawuran kamfen.

Tsauri wanda ya ke magana a helkwatar jam’iyyar a Abuja, ya ce duk jihar da gwamnan PDP ya kaura zuwa APC kamar Zamfara da Kuris Ribas, to ba shakka PDP za ta lashe zabe a jihar a zaben mai zuwa.

Sanata Tsauri ya yi zargin cewa barazana ce ga wasu gwamnonin kan sa su rikicewa su fice daga PDP zuwa APC.

Babban sakataren na adawa ya ce ya na mamakin yanda wadanda a ke zargi a PDP da zarar sun koma APC sai a ba su mukami da misalin tsohon gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio.

Tsauri ya ce ba don hukuncin kotun koli cewa APC ce ta lashe zaben 2019 , da sai ya ce ba ko tantama PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar ta lashe zaben.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *