• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUN IYA BAKIN KOKARIN MU WAJEN INGANTA LAMURAN NAJERIYA-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa ta sauya lamuran yanda Najeriya ta tabarbare gabanin hawan sa mulki a 2015.

Shugaban wanda ya ke zantawa da gidan talabijin na Najeriya NTA ya ce har yanzu ya na kan bakar sa na a kirkiro kotuna na musamman na hukunta masu cin hanci da rashawa don a samu saurin yanke hukunci kuma mutane su san gwamnatin da gaske ta ke yi.

Shugaban ya koka yanda masu almundahana ke amfani da lauyoyi wajen jan shari’a a shafe shekaru har ma wani alkalin Allah ya karbi abun sa ba tare da kammala shari’a ba.

Shugaban ya ce ya samu nasarar yin allurar korona bairos ta biyu don haka ma ya huta da sanya takunkumi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.