• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUN FARA RABAWA NAKASASSU NAIRA DUBU BIYAR-BIYAR A WATA-HUKUMAR NAKASASSU

ByYusuf Yau

Oct 23, 2021

Hukumar kula da walwalar nakasassu ta Najeriya ta baiyana cewa ta fara rabawa nakasassu dubu 50 naira dubu biyar-biyar duk wata inda tuni har wasu sun fara ganin sakon kudin ta asusun sun a banki.
Shugaban hukumar James David Lalu ya ce wannan tsari zai cigaba da wanzuwa har lokacin da Allah ya hukunta kuma nan gaba za a iya samun kara yawan wadanda za su ci gajiya.
Lalu ya kara da cewa an zabi wadanda ke cin gajiya daga dukkan jihohin Najeriya kuma ba a nuna son kai tsakanin maza ko mata ko bambancin siyasa ba.
Shugaban hadaddiyar kungiyar nakasassu Abdullahi Aliyu Usman ya ce ya bincika 鈥榶an kungiyar sa daga Kebbi, Bayelsa, Akwa Ibom, Binuwai, Gombe da Yobe sun fara samun kasafin.
Yanzu dai za a jira a ji rahoto daga sauran jihohi da kuma dorewar tura kudin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI馃榾馃榾馃榾
One thought on “MUN FARA RABAWA NAKASASSU NAIRA DUBU BIYAR-BIYAR A WATA-HUKUMAR NAKASASSU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.