• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUN CAFKE MUTUM 12 DA KE DA HANNU A LAMURAN TAIMAKAWA SATAR JARRABAWAR AFURKA TA YAMMA – RUNDUNAR ‘YAN SANDA

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta damke mutum 12 da ke da hannu wajen taimkawa satar jarrabawar Afurka ta yamma da a ka gudanar kwanannan.

A sanarwa daga kakakin rundunar na kasa Frank Mba, ta baiyana cewa an kama mutanen don amfani da matsayin su na jami’an kula da jarrabawar wajen taimakawa satar jarrabawa.

An cafke mutanen a jihar Kano, Nassarawa, Kano, Bauchi da Ribas.
Mutanen sun hada da Dayo West, Shalom Essien, Anyanwu Precious, Hanson Beloved, Ali Musa, Umar Mohammed, Isa Abdullahi, Hamisu Hussaini Abdullahi, Maharazu Sabo, Yusuf. M. Mailafiya, Sule Bukata Garba da Wudana K. Solomon.

Mutanen sun yi amfani da hanyoyi ciki har da na yanar gizo wajen ba da amsa ga dalibai.

Rundunar ta ce ta dau matakin ne don karfafa ingancin lamuran jarrabawar ta kammala sakadandare.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “MUN CAFKE MUTUM 12 DA KE DA HANNU A LAMURAN TAIMAKAWA SATAR JARRABAWAR AFURKA TA YAMMA – RUNDUNAR ‘YAN SANDA”
 1. Hey there! I know this is kind of off topic but I was
  wondering if you knew where I could locate a captcha plugin for my comment
  form? I’m using the same blog platform as yours and I’m
  having difficulty finding one? Thanks a lot!

 2. Wonderful work! That is the type of info that should be shared
  around the web. Shame on the search engines for now
  not positioning this publish higher! Come on over and consult with my website .
  Thanks =)

Leave a Reply

Your email address will not be published.