Fadar gwamnatin Najeriya Aso Rock ta ce ta bankado shirin batanci ga shugaba Buhari da nuna ba ma shi ya ke mulkin Najeriya ba.
Kakakin shugaba Buhari wato Femi Adeshina ya baiyana haka a wata sanarwa da ke cewa za a yi amfani da kafofin yanar gizo don yada wannan kamfen din a kwanaki masu zuwa.
Adeshina ya ce za a yi amfani da wata kafa ta ketare wajen yada wannan batanci da wasu makiyan shugaban ke zugawa da daukar nauyi.
Duk da sanarwar dai ba ta ambaci sunan kafar ba ko kai tsaye masu daukar nauyin, amma ta ce wasu lalatattun ‘yan siyasa ne.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀