• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUN BA WA OBIANO BELI AMMA BAI CIKA SHARUDA BA TUKUN-EFCC

Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya EFCC ta baiyana cewa ta amince da ba da belin tsohon gwamnan Anambra Willie Obiano amma bai cika sharuda ba tukun.
Obiano dai ya shiga hannun hukumar yayin da ya ke hanyar ficewa daga Najeriya bayan mika ragama ga sabon gwamna Charles Soludo.
Shugaban hukumar ta EFCC Abdulrashid Bawa ya ce hukumar ba za ta fitar da bayanan tuhumar Obiano ba don kaucewa zargin ta na yayata asiran mutane a kafafen labaru da zummar bata mu su suna.
Kazalika Bawa ya musanta cewa kama Obiano na da nasaba da siyasa da kuma bita-da-kulli.
Jam’iyya Obiano APGA ta zargi EFCC da bugewa da siyasa wajen kama tsohon gwamnan wanda ya samu wa’adi biyu a karagar gwamnatin Anambra.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “MUN BA WA OBIANO BELI AMMA BAI CIKA SHARUDA BA TUKUN-EFCC”
  1. Hi there, You’ve done a fantastic job. I will definitely digg it and for my part recommend to my friends. I am confident they’ll be benefited from this site.

Leave a Reply

Your email address will not be published.