• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUN BA DA SABON WA’ADI KAN MAKOMAR DALIBAN GREENFIELD-MADUGUN BARAYI

Madugun barayin da su ka sace daliban jami’ar Greenfield wato Sani Idris Jalingo da a ke yi wa lakabin BALERI ya ce sun sake sabon lokacin wa’adi ga makomar rayuwar daliban zuwa Larabar nan.

A zantawa ta wayar tarho daga maboyar su da ba a tantance ba, Baleri ya ce wasu mutane sun sa baki don su sassauta mugun abun da su ka yi niyya kan yaran, don haka su ka janye daukar matakin zuwa Larabar nan.

In za a tuna barayin sun bukaci diyyar Naira miliyan 100 duk da tuni an ba su Naira miliyan 55 amma sun ce wannan sun kashe wajen sayawa yaran abinci.

Akwai dalibai 17 a hannun barayin bayan tun farko sun yi kisan gilla kan dalibai 5.

Baleri wanda ya ce ba da wasa ya ke magana ba, ya karfafa fatar samun abun da su ka bukata a safiyar Larabar nan, ko kuma in hakan bai yiwu ba su cutar da daliban.

Tun fitowar labarin barazanar a ranar litinin, mutane ke nuna zullumin su na abun da zai iya faruwa da shiga addu’ar samun mafita daga yanayin mai ban tsoro.

Gwamnatin jihar Kaduna na kan bakanta na ka da a cigaba da ba da kudin fansa don hakan tamkar karfafawa barayin guiwa ne su cigaba da sana’ar ta rashin imani.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.