• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUKTARI SALEH YA KAMA HANYAR ZAMA SABON SARKIN MAKAFIN ABUJA

ByNoblen

Jan 31, 2022

Kakakin hadaddiyar kungiyar makafin arewacin Najeriya Muktari Saleh ya kama hanyar zama sabon sarkin makafin babban birnin taraiyar Najeriya Abuja.
Saleh ya samu tagomashin bayan rasuwar aminin sa marigayi sarkin makafin Abubakar Umar.
Rahotanni sun baiyana cewa a cikin kuri’u 16 da aka kada na zaben sabon sarkin, Mukhtari Saleh na da kuri’u 12.
A yanzu haka a na jiran tabbatar da sarautar ce daga sarkin Garki Nda Kufe da ke kula da sarautar cikin birnin Abuja.
Kazalika an samu labarin iyalan marigayi sarkin makafi Umar sun zo wajen Mukhtari su ka ma sa mubaya’a don ganin yanda ya zauna lafiya da marigayi.
An ga Mukhtari Saleh a wajen taron wata-wata na kungiyar ma’abota kafafen labaru don cigaban kasa a Abuja.
A lokacin taron an ba da kyautuka ga wadanda su ka yi hazaka a fadakarwa da kuma yada labaru a kungiyar da su ka hada da Malam Isa mai darasin “HASKEN MAKARANTA” sai Ibrahim SD Kusfa da darasin san a “LABARUN DUNIYA”

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
36 thoughts on “MUKTARI SALEH YA KAMA HANYAR ZAMA SABON SARKIN MAKAFIN ABUJA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.