• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUHAWARAR YANKIN DA ZAI FIDDA SHUGABA A 2023 NA KARA ZAMA ABUN ZANTAWA TSAKANIN MANYAN ‘YAN SIYASA

ByNoblen

Jan 11, 2022 ,

Muhawarar yankin da zai fidda dan takarar shugaban kasa tsakanin manyan jam’iyyu na APC da PDP na zama babban abun tattaunawa tsakanin manyan ‘yan siyasar Najeriya.
Yayin da akasarin ‘yan kudu ke cewa lalle dan takarar ya fito daga yankin su, ‘yan arewa na da bambancin ra’ayin abar takarar a bude kowa ya gwada karbuwar sa.
A zantawa da a ka yi da shugaba Buhari da gidan talabijin na Channels ya nun aba zai baiyana dan takarar da zai marawa baya ba don gudun kar a ma sa makarkashiya, da hakan ma ya nuna ba bukatar tambayar sa dan takarar na sa daga arewa ya ke ko kudiu.
A na raderadin irin su Bola Tinubu, Goodluck Jonathan da ma mataimakin shugaban Yemi Osinbajo ka iya zama a jerin wadanda a ke tsammani ke da tagomashi.
Ga babban dan siyasa Bamanga Tukur, barin takarar a bude shi ya fi dacewa da tsarin dimokradiyya.
A na sa bangaren tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau, ya ce ba laifi in an ba wa kudu dama su fitar da dan takara.duk da ya na takaicin yanda ‘yan siyasar kudu ke zakewa cewa lallae lokacin su ne na shugabancin kasa.
A duk lokacin da gwamnoni ke ‘yan siyasar kudu ke magana na nuna mulki na su ne bayan kammala wa’adi biyu na shugaba Buhari.
Nan ma tsohon ministan aiyuka ne Adeseye Ogunlewe ke cewa lokaci ya yi da arewa za su yi mu su kara su bar mu su tikiti.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
11 thoughts on “MUHAWARAR YANKIN DA ZAI FIDDA SHUGABA A 2023 NA KARA ZAMA ABUN ZANTAWA TSAKANIN MANYAN ‘YAN SIYASA”
  1. Do you mind if I quote a couple of your articles as long as I provide credit and sources
    back to your website? My blog is in the very same area of interest as yours and my visitors would certainly benefit from a lot of the information you provide here.
    Please let me know if this okay with you. Regards!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *