• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU’AZU MUHAMMAD KWAIRANGA YA ZAMA SABON SARKIN FUNAKAYE

Mako daya bayan rasuwar daya daga manyan sarakunan jihar Gombe, Sarkin Funakaye, gwamnan jihar ya nada Mu’azu Muhammad Kwairanga a matsayin sabon sarki.

Masu gadon sarauta a Funaye ‘yan uwan fadar Gombe ne kuma jikokin Modibbo Babayero wanda ya karbo tuta daga Shehu Usmanu Dangodio.

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Dasuki Jalo ya mika takardar nadin sabon sarkin a helkwatar masarautar wato garin Bajoga da ke arewacin jihar Gombe kan hanyar Potiskum a jihar Yobe.

Jalo ya ce cikin wadanda su ka nemi sarautar su 3, Allah ya ba wa Mu’azu don haka ya bukaci a mara masa baya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
41 thoughts on “MU’AZU MUHAMMAD KWAIRANGA YA ZAMA SABON SARKIN FUNAKAYE”

Leave a Reply

Your email address will not be published.