• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU YI ADDU’AR HADIN KAN NAJERIYA A LOKACIN SALLAH-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar musulmi su yi amfani da lokacin babbar sallah wajen taya Najeriya addu’ar dorewar hadin kai da zaman lafiya.

A sakon sa na idin karamar sallah, shugaban ya nuna takaicin yanda wasu tsageru su ka zabi kai wa jami’an tsaro hari a yankin kudu maso kudu da kudu maso gabar.

Wannan muguwar dabi’a ta sa shugaban yin jirwaye mai kamar wanka cewa idan an cigaba da nakkasa jami’an tsaro ta kai mu su hari, to ya ya za a yi kenan ranar da za a bukace su in lamura su ka rikice?.

Shugaban ya bukaci shugabannin addini, na al’umma da sarakunan gargajiya su jagoranci al’umma bisa abun da zai taimakawa hadin kan kasa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.