• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA YABAWA TAMBUWAL DA JANYEWA DON ATIKU-DODO OROJI

ByMardiya Musa Ahmed

May 31, 2022

Tsohon shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta miyetti Allah a Abuja Muhammad Dodo Oroji ya yabawa gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal don janye takarar da ya yi ta neman tikitin PDP ya mara baya ga Atiku Abubakar.

A zantawa da kafar labarum ketare, Oroji ya danganta janyewar da kwarewar siyasa da hakan ya sa a ka samu wanda ya lashe zaben da kuri’u masu yawa maimakon raba kuri’u kalilan ga kowane daga ‘yan takarar.

Oroji ya ce tsayar da Atiku da PDP ta yi ya sa ya zama wajibi ga APC ta yi dogon nazari wajen tsayar da dan takarar da zai iya tinkarar Atiku a babban zaben 2023.

Dattijon ya bukaci dukkan manyan jam’iyyu su yi siyasar ba tare da dabi’ar ko a mutu ko a yi rai ba don yanda a yanzu a ke fama da kalubalen tsaro a sassan Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.