• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA TARE DA ISA PANTAMI-FADAR ASO ROCK

Fadar gwamnatin Najeriya Aso Rock ta ce ta na tare da ministan sadarwa Isa Ali Pantami kan yanda ya ke bunkasa harkokin sadarwa da tattalin arziki.

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu a wata sanarwa, ya ce gwamnatin ta gamsu da yanda ministan ya dage wajen rage farashin damar hawa yanar gizo ga talakawa.

Sanarwar martani ne ga wani kamfen din batunci ga ministan da wasu ke yadawa na nuna ya yi wasu kalamai a baya na mara baya ga tsaurin ra’ayi.

Garba Shehu ya ce lokacin da ministan ya yi irin wadannan kalaman ya na matashi a shekarun sa na 20, kuma ya janye ra’ayoyin, inda a badi zai cika shekara 50 a duniya.

Ra’ayin na fadar Aso Rock na nuna ba daidai ba ne yanda masu sukar ke yada lamura da su ka shude don ruguza darajar wani.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MU NA TARE DA ISA PANTAMI-FADAR ASO ROCK”
  1. I really like your blog.. very nice colors & theme.
    Did you design this website yourself or did you hire someone to
    do it for you? Plz respond as I’m looking to construct my own blog and would like
    to find out where u got this from. appreciate it

Leave a Reply

Your email address will not be published.