• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA SON ‘YAN MAJALISA SU SAKE TUNANI KAN KUDURIN DOKAR MATAKI KAN KUDIN FANSA-IMAM ABUBAKAR LAMIDO

Shehun malamin Islama Imam Abubakar Lamido ya bukaci ‘yab majalisar dokokin Najeriya su sake tunani wajen kudurin dokar daukar mataki mai tsauri kan wanda ya ba da kudin fansa don ceto dan uwan sa daga hannun masu satar mutane.

Imam Lamido wanda ke gabatar da hudubar jumma’a a masallacin Bolar, Gombe, ya na magana kan tarukan ra’ayoyin jama’a don gyaran kundin mulkin kasa inda tun gabanin hakan kudurin daukar mataki kan mai ba da kudi don fansar dan uwan sa ya taso.

Malamin ya ce maimakon a ji cewa an kawo kudurin daukar matakin magance masu satar mutane, amma sai a ka kawo mataki bayan an kyale an sace mutanen da hakan ke nuna an bar muhimmin matakin hana satar an koma tamkar yi wa wadanda a ka sace ‘yan uwan su barazana.

Limamin ya bukaci daukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma maimakon zarewa ‘yan kasa ido su bar ‘yan uwan su a hannun masu satar wai har masu satar su gaji su daina.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MU NA SON ‘YAN MAJALISA SU SAKE TUNANI KAN KUDURIN DOKAR MATAKI KAN KUDIN FANSA-IMAM ABUBAKAR LAMIDO”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *