• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA SON KASHI 50% NA MUKAMAI TSAKANIN MU DA GWAMNATIN ZAMFARA-YARI

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya ce su na bukatar kashi 50% na rabon mukamai da na jam’iyya tsakanin su da gwamnatin Zamfara.

Wannan ya biyo bayan sauya sheka da gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya yi ne daga PDP zuwa APC da hakan ya ba shi damar amshe ragamar jam’iyyar APC.

Abdul’aziz Yari a zantawar sa da manema labaru a Abuja, ya ce rabon na kashi 50% ne zai ba wa huldar su da sashen gwamnan nasara da jituwa.

In za a tuna Yari da Sanata Kabiru Marafa ba su amince da amshe ragamar jam’iyyar APC ta Zamfara don Maradun ya dawo cikin ta.

Yanzu za a jira martanin gwamnatin Zamfara da ba ta kan matsayar rabon ya kai wannan yawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MU NA SON KASHI 50% NA MUKAMAI TSAKANIN MU DA GWAMNATIN ZAMFARA-YARI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.