Tsohon ministan cikin gidan jamhuriyar Nijar Idi Ango Umarou ya bukaci shugaban kasar Bazoum Muhammed ya maida hankali wajen neman dabarun magance kalubalen tsaro daga cikin gida maimakon tura dukkan lamura ketare.
A zantawar sa da Muryar Amurka a Yamai, tsohon ministan ya ce girka zaman lafiya sai da ‘yan kasa don a na yi mu su kirari da “sai da dan gari a kan ci gari.”
Ba mamaki Umarou na nuna damuwa ga yanda sabon shugaban ke neman mafitar kalubalen tsaron kasar daga ketare.
Ra’ayin Umarou ya zo daidai da na tsohon ministan matasa da wasanni na Najeriya Solomon Dalung da ke ba da shawara ga gwamnatin shygaba Buhari da ka da ta dau shawarar masu cewa a nemo dakarun kasashen ketare su shigo don taimakawa a yaku miyagun iri.
Dalung ya ce matsalar Afurka sai jama’ar Afurka ne za su iya magance ta, don da zarar an shigo da wasu daga turai to za su raina kasar ne ko a shiga kallon kallo tsakanin su da dakarun gida da za su iya daukar an raina kuruwar su.