• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA SON A YI GARAMBAWUL A LAMURAN TSARON AREWACIN NAJERIYA-GAMAIYAR KUNGIYOYI

Gamaiyar kungiyoyin matasan arewa CNG ta bukaci garambawul ga lamuran tsaron yankin arewa da ya tabarbare har ya kai ga mutane ba sa barci da ido biyu a rufe.

A sanarwa daga kakakin kungiyar Abdulaziz Suleiman, kungiyar ta nuna rashin gamsuwa ga matakan da gwamnatin taraiya ke dauka wajen murkushe miyagun iri.

CNG ta lissafa kalubalen satar mutane, Boko Haram da illar ‘yan bindiga dadi a matsayin annobar da ta addabi yankin na arewa.

Karshe dai kungiyar ta ce babban zabi shi ne jama’a su rika hada kai su na kula da lamuran tsaron su don gwamnati ita kadai ba za ta iya kawo dukkan tsaron da a ke bukata ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.