• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA SON A RAGE MA NA HARAJI-KANANAN ‘YAN KASUWA A NIJAR

Kananan ‘yan kasuwa a jamhuriyar Nijar na bukatar rangwamen kudin haraji daga hukumomin kasar don ririta jarin su.

Taron shugabanin ‘yan kasuwar jamhuriyar Nijar da ya gudana a karshen mako a birnin Yamai ya bukaci gwamnatin kasar da kungiyoyin duniya masu kula da sha’anin kasuwanci su gudanar da bincike don tantance harajin da ya dace a dorawa kananan ‘yan kasuwa, don tsadar haraji ke barazanar durkusar da harakokin ‘yan kasuwa masu karamin jari.

Shugaban  kungiyar ‘yan kasuwa ta SIEN Alhaji Yakouba Dan Maradi ya baiyana wannan bukata, ya na mai cewa harajin yafi karfin jarin da ‘yan kasuwar ke amfabi da shi wajen odar kayan masarufi.

Duk da kungiyar ta SIEN ta dillalan shigo da kaya ne daga ketare, Alhaji Yakouba ya ce duk wadannan na ajin kananan ‘yan kasuwa don harkar kasuwanci ta shafi dukkan ‘yan kasuwa.

Yakouba ya ce duk ‘yan kasuwar na bukatar rangwamen da hakan ma ya sa su ka turo wakilan su taron.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
59 thoughts on “MU NA SON A RAGE MA NA HARAJI-KANANAN ‘YAN KASUWA A NIJAR”
  1. obviously like your website but you have to check the spelling on several of your posts. Many of them are rife with spelling issues and I to find it very bothersome to inform the truth then again I’ll surely come back again.

Leave a Reply

Your email address will not be published.