• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA SON A KORI SHUGABAR HUKUMAR DAIDAITON DAUKAR MA’AIKATA TA NAJERIYA DON SABA DOKA-MATASA

Gangamin matasa bisa jagorancin tsohon shugaban  majalisar matasa ta Najeriya NYCN ya taru a gaban hukumar kula da daidaiton daukar aiki a Abuja don neman shugaba Buhari ya kori shugabar hukumar Muheeba Dankaka daga ofis don zargin son zuciya kan daukar ma’aikata.

Matasan rike da kwalaye na zargin almundahana, sun zaiyana Dankaka da cewa ba ta cancanci zama a kujerar ba ko na wuni daya ne.

Cikin zargin da ‘yan zanga-zangar su ka yi akwai yanda Muheeba Dankaka ke dagawa ma’aikatu kafa su dauki ma’aikata daga inda su ka ga dama ba tare da sauran sassan kasa sun amfana ba.

Hakanan sun ce Dankaka na da dagun kai da mulkin kama-karya da hakan ke hana dubban matasa da su ka gama makaranta samun guraben aiki.

Jagoran zanga-zangar Komred Murtala Garba, ya ce sun ba da nan da mako uku Dankaka ta yi murabus ko shugaba Buhari ya sallameta daga aiki, don in ba haka ba za su mamaye helkwatar hukumar da yin zaman dirsham.

A martanin hukumar ta bakin kwamishina mai wakiltar Bayelsa Sir Tonye Okiyo ya nemi shashantar da zargin da nuna cewa ba hurumin hukumar ba ne daukar ma’aikata.

Hakanan Okiyo ya ce ai shugaba Buhari ya turo mu su Muheeba da ta ke uwa ce a gare su kuma ta yi abun da ba a yi ba a baya na raba mu su motocin aiki.

A watan Febreru 20 cikin kwamishinonin hukumar 37 sun rubuta korafin zargin Dankaka da murdiya wajen daukar ma’aikata a hukumar inda ta fifita ‘yar jihar ta ta Kwara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
63 thoughts on “MU NA SON A KORI SHUGABAR HUKUMAR DAIDAITON DAUKAR MA’AIKATA TA NAJERIYA DON SABA DOKA-MATASA”
  1. Ahaa, its fastidious dialogue regarding this post at this place at this weblog, I have read all that, so now me also commenting here.

  2. Heey there! Do you use Twitter? I’d like to follow you if that would be okay.

    I’m undoubtedly enjoying your blog and look forward to new posts.

    JKR investors homepage investment fund

Leave a Reply

Your email address will not be published.