• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA SO SHUGABANNI SU ZAMA MASU ADALCI – MA’ABOTA KAFAFEN LABARU

Kungiyar ma’abota kafafen labarun Najeriya ta bukaci shugabanni musamman na siyasa su kaucewa alkawarin zane kan ruwa don tarihi ya mu su adalci.
Kungiyar da ta hada da masu sauraron rediyo da kallon talabijin har ma da masu karanta jaridu, ta ce duk alkawarin da ‘yan siyasa ke yi na nan a ajiye a kundin bayanai na rubutu ko na faifayin sauti da na bidiyo.

Shugaban kungiyar matashi Buhari Yunusa Kumurya ya ce a taron ta na wata-wata a lahadin nan a Abuja, kungiyar za ta yi bitar wasu alkawuran da ‘yan siyasa su ka dauka da duba sun cika ne ko har yanzu gafara sa a ke ji ba a ga kaho ba.

Kumurya ya ce wadanda ba sa cika alkawari kar su yi tsammanin cewa ko ba a hukunta su a duniya da hujjojin dan adam ba, za su kuma iya yin wata dabara ko buya a ranar gobe kiyama.

Kungiyar ta bukaci kowa ya duba kan sa ya ga abun da ya ke yi da ba daidai ba ya gyara kafin lokaci ya kure; hakanan in mutum ya fahimci ya na wata dabi’a mai kyau sai ya kara azama.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.