• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA SO KU FADA MA SUNAN ‘YAN ZANGA-ZANGAR NEMAN KASAR ODUDUWA-KWAMISHINA

Kwamishinan ‘yan sanda na Lagos Hakeem Odumosu ya bukaci bayanan duk wadanda su ka taru don yin zanga-zangar neman kafa kasar Yarbawa a dandalin Gani Fawehemmi da ke Ojota a Lagos.

Rashin wadannan bayanai ya sanya daga bisani ‘yan sandan da su ka yi dafifi a dandalun su ka tarwatsa taron da borkonon tsohuwa da ruwan zafi.

Hakeem ya yi jawabi ne ga manema labaru kafin fara zanga-zangar da dan bangar Yarbawa Sunday Igboho ya shirya wacce kuma ta tara kamar mutum 100.

Kwamishinan ya ce wasikar da ‘yan zanga-zanga su ka aiko ba ta kunshi duk bayanan da a ke bukata ba da su ka hada da wajen da za a yi zanga-zangar.

Bayan tarwatsa zanga-zanga an samu labarin kama akalla mutum biyu mace da namiji da a ka ce sun dorawa motar su kellen alamun kasar ta Oduduwa.

Kazalika an yayata cewa wata mata ta rasa ran ta don harsashi ya yi batan kau ya same ta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2,556 thoughts on “MU NA SO KU FADA MA SUNAN ‘YAN ZANGA-ZANGAR NEMAN KASAR ODUDUWA-KWAMISHINA”