Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya IPMAN ta baiyana cewa ta na mara baya ga cire tallafin man fetur da gwamnatin Buhari ke shirin yi a badi.
Shugaban kungiyar Chinedu Okoronkwo ya shaidawa kamfanin dillancin Najeriya matsayar ta su.
IPMAN ta ce dokar gyara sashen man fetur da shugaba Buhari ya rantaba hannu ba ta kunshi kudin tallafin fetur ba.
Hakanan kungiyar ta ce tallafin ba ya amfanin masu harkar fetur a cikin kasa wato ma’ana sai masu shigo da man daga ketare.
‘Yan kasuwar sun ce su na fatan in an cire tallafin za a ba da damar kasuwa ta yi halin ta tsakanin masu sayar da man.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
❤️ Alice sent you a HOT video! Click Here: http://bit.do/fSHAz ❤️