• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA KIRA GA GWAMNATIN FILATO TA SASSAUTA DOKAR HANA FITA-ALI ABDULLAHI

Wani shaharerren dan jarida kuma mai sharhi Mallam Ali Abdullahi ya bukaci gwamnatin jihar Filato ta sassauta dokar hana mutane fita dare da rana a karamar hukumar Jos ta arewa.

Ali Abdullahi wanda ya ke juyayin zubar da jinin wadanda ba su yi laifin komai ba a jihar, ya ce zafin zama a gida ba zai kawo warakar fitinar Filato ba; don haka gara a rage dokar da rana mutane su rika samu su na fita neman na cefane hakanan marar sa lafiya su rika tafiya asibiti.

Dan jaridar ya ce halin kunci da mutane kan shiga na da mummunar illa kan jama’a kuma wani nau’i ne na fitina.

A ganin Ali Abdullahi, gwamnati za ta ita rage tsawon lokacin hana fita ta sa jami’ai su rika sintiri don tabbatar da doka da oda.

Abdullahi ya ce babbar hanyar magance fitinar ita ce Hukunta duk wanda a ka samu da laifi don ya zama darasi ga sauran masu son yi wa doka karantsaye.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.