• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA GOYON BAYAN TABBATAR DA ‘YANCIN UKRAINE-KASAR CYPRUS

ByNoblen

Mar 2, 2022 , ,

Ministan harkokin wajen Cyprus ya ce ra’ayin kasar sa ya zo daya da na sauran kasashen taraiyar turai da ke mara baya ga cin gashin kasar Ukraine ta hanyar kare kan iyakokin ta da na sauran kasashe.
Ministan mai suna Loannis Kasaoulides na magana ne a zantawa ta musamman da jaridar ARAB NEWS ta Saudiyya.
Kasoulides ya kara da cewa ba hujja ba ce sauran Ukraine ya shafu don gashin kan arewacin kasar da kasar Turkiyya ce kadai ta amince da bantarewar sa daga kasar.
Kasancewar Cyprus na da dangantaka ta kusa da Rasha da Ukraine ya zama a na zuba ma ta ido kan matakan da za ta dauka kan mamaye Ukraine da Rasha ta yi.
Cyparus mai mutum miliyan 1.22 na dogara ne ga lamuran yawon bude ido da Ukraine da Rasha ke karfafawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
50 thoughts on “MU NA GOYON BAYAN TABBATAR DA ‘YANCIN UKRAINE-KASAR CYPRUS”

Leave a Reply

Your email address will not be published.