• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU NA FATA ZA A SAMU GUDANAR DA AIKIN HAJJI NA BANA-NAHCON

ByYusuf Yau

Nov 22, 2021

Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta ce ta na fata da yardar Allah za a gudanar da aikin hajjin bana hijra.

Jami’ar labarun hukumar Fatima Sanda Usara ta ce su na zuba ido kan nasarorin da a ke samu a Saudiyya da ke da kwarin guiwar yiwuwar gudanar da aikin hajjin.
Duk da haka NAHCON ba za ta ce za ta fitar da jadawalin rejistar alhazai don duba abun da ya faru a baya amma hukumar za ta cigaba da duba lamura don daukar matakin da ya dace kan shirye-shiryen aikin hajjin.
NAHCON ta ce ta na ganin hukumomin alhazai na jihohi ma za su fara wasu shirye-shirye na wucin gadi don in Allah ya sa za a gudanar da aikin a samu sauki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.