• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

MU NA DA WADATACCEN MAN FETUR KUMA MUN JANYE MUMMUNAN MAI DAGA KASUWA-HUKUMAR FETUR TA TUDU

Hukumar kula da man fetur na cikin kasa ta Najeriya ta baiyana cewa ta na da wadataccen man fetur da zai wadatar da jama’a, don haka ba bukatar wata fargaba.
Da alamu hukumar na kokarin kwaranye fargabar jama’a ne na shiga yanayin karancin man da kuma korafin shan mai marar inganci mai kawo illa ga motoci da babura.
Hukumar ta cigaba da cewa ta janye mummunan mai da a ka shigo da shi a kasuwa don haka a ka samu gibin kwana 10 na wadatar man amma a na da man da zai ishi jama’a na kwana 20.
Ma’ana hukumar na cewa a yanzu an yi odar mai kwatankwacin yawan wanda a ka janye a kasuwa, don haka daidaita wannan gibin kan haddasa karancin sa da kan jawo layuka a gidajen man musamman Abuja da Lagos.
Da alamu ba wata diyya da za a biya mutane da su ka samu matsala a motocin su sanadiyyar shan jirkitaccen man.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MU NA DA WADATACCEN MAN FETUR KUMA MUN JANYE MUMMUNAN MAI DAGA KASUWA-HUKUMAR FETUR TA TUDU”
  1. I’m writing on this topic these days, bitcoincasino, but I have stopped writing because there is no reference material. Then I accidentally found your article. I can refer to a variety of materials, so I think the work I was preparing will work! Thank you for your efforts.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *