• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU MIKA WUYA GA MATAWALLE-INJI AMINU SANI JAJI

Daya daga mutum 8 da su ka nemi tikitin takarar gwamna a APC a jihar Zamfara Aminu Sani Jaji ya bukaci sauran abokan tafiyar sa, su mika wuya ga gwamnan jihar Bello Matawalle wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Sani Jaji na magana ne kan nuna rashin amincewa da rushe shugabancin jam’iyyar APC a jihar inda a ka damka ragamar ta ga gwamnan PDP da ya dawo APC.

Tsohon gwamann jihar wanda shi ne tsohon jagoran jam’iyyar ya nuna rashin gamsuwa da matakin da uwar jam’iyyar karkashin gwaman Mai Mala Buni ta dauka.

Hakanan shi ma Sanata Bello Marafa ya nuna sam ba za su amince da matakin jam’iyyar na kasa ba sai in an sake lale.

Kabiru Marafa na kan gaba a lokacin da ‘yan takarar na APC su ka bijirewa tsohon gwamnan a zaben da Kogunan Gusau ya lashe amma hukuncin kotu ya sa PDP ta haye dukkan kujeru.

Sani Jaji ya ce Allah ke ba da mulki don haka ya na ganin bin Mawallen Maradun shi ne maslaha da kuma amincewa da kaddara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *