• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MU KAN BIYA HAR NAIRA BILIYAN 12O DUK WATA DON SAMUN RANGWAMEN LITAR FETUR-NNPC

Kamafanin man fetur na Najeriya NNPC ya ce ya kan kashe tsakanin Naira biliyan 100-120 duk wata don samun farashin litar fetur ya zama da rangwame a kasar.

Shugaban kamfanin Mele Kyari Kolo ya baiyana cewa asalin litar daga yanda a ke shigo da man da iso da shi kan tashi kan Naira 234 da hakan ya nuna gwamnati na yin rangwame a sayar da litar kan Naira 162.

Gwamnatin dai ta sha nuna ta janye duk wani tallafi don ta na daukar tallafi a matsayin hanya ta cin hanci da rashawa.

Kolo Kyari ya ce nan gaba dole ya kai ga ‘yan Najeriya na biyan asalin farashin litar ta mai don gwamnati ba za ta cigaba da jurewa biyan kudi don wannan rangwamen ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *