• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MOTOCI SUN YI HATSARI A SASSA DABAN-DABAN NA AREWA MASO GABAR

ByNoblen

Dec 18, 2021 ,

An ga motoci a sassan arewa maso gabar sun yi hatsari da ya shafi wa imma taho-mu-gama ko gugar juna da ya shafi lafiyar ma’abota motocin da ma ragargaza motocin.
Yawan hatsarin ba zai rasa nasaba da yawan tafiye-tafiyen jama’a a karshen shekarar miladiyya ta 2021 da kuma ganganci a tuki.
Kazalika wani dalilin ya shafi yanda titunan ke da ramuka masu muni don gyare-gyaren da a ke yi ba su karade dukkan inda a ke bukata ba.
An ga jami’an kare aukuwar hatsura na tsaya a sassa daban-daban daf da madakatun motoci da sojoji ko ‘yan sanda ke kula da su.
Hakanan a yankin nan na FOREST kan hanyar Akwanga zuwa Jos, alkalin tafi da gidan ka na kula da laifukan direbobi ya fito da cin tarar direbobin da musamman su ka yi lodi da ya wuce kima.
Duk da haka wasu direbobin kan zullewa biyan tarar duk da laifukan da su ke aikatawa.
 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MOTOCI SUN YI HATSARI A SASSA DABAN-DABAN NA AREWA MASO GABAR”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *