• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MOTAR BARASA TA KATSE ABUJA DA KE JIHAR NASSARAWA NA TSAWON SA’O’I DA DAMA

Hatsarin mota shake da barasa ya katse saukin zirga-zirga tsakanin babban birnin Najeriya Abuja da jihar Nassarawa.
Duk masu yunkurin fita daga kokuwar Abuja zuwa yankunan Nassarawa da ke makwabtaka da ma wasu jihohin arewa ta tsakiya da arewa maso gabar sun makale na tsawon sa’o’I 7 don jiran budewar hanyar.
Toshewar hanyar ya sa wasu bin hanyar shigowa da hakan ya kara cakuda tagwayen titunan,
Wasu ma’abota yanar gizo da ke cikin wadanda su ka makale sun yi kokarin sanar da jama’a halin da a ke ciki don kaucewa bin hanyar.
Kalubalen ya zo daidai lokacin daura auren wani matashi Ibrahim SD Kusfa Zaria a anguwar Masaka inda ala tilas masu karbar aure su ka dale babura don sama tafiyar ba za ta yiwu ta mota ba.
Kabiru Idris na Muryar Ma’abota kafafen labaru da ya dauko tawaga zuwa auren ya makale, ya rasa tawagar ta sa don kowa ya nemi hanyar tafiya auren ta hanyar hawa babura da ke da ganganci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MOTAR BARASA TA KATSE ABUJA DA KE JIHAR NASSARAWA NA TSAWON SA’O’I DA DAMA”
  1. I’m not sure where you’re getting your info, but good topic.
    I needs to spend some time learning more or understanding more.
    Thanks for wonderful info I was looking for this information for my
    mission.

Leave a Reply

Your email address will not be published.