Mai ba wa shugaban Najeriya Buhari shawara kan tsaro Manjo Janar Babagana Monguno ya kira taron cibiyar yaki da damfarar yanar gizo don yi ma ta cajin batur kan kalubalen.
Monguno ya kira taron ne don yanda korafi ke karuwa na yanda ‘yan damfarar ke haddasa cikas ko cin karen su ba babbaka.
An kirkiro cibiyar a 2016 don aiwatar da dokar yaki da damfarar da a ka amince da ita a 2015.
An gano cewa cibiyar ba ta faye zama don kula da wannan aiki ba da a baya a ke ganin tamkar Najeriya ba ta fara samun tsanantar wannan kalubalen ba.
A kwanakin nan hukumar yaki da cin hanci EFCC ta aiyana yankin Lekki a Lagos da zama tungar ‘yan damfarar yanar gizo.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀