• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MIYAGUN IRI SUN YI SANADIYYAR RASA RAN SOJA DA KUMA SACE MATA DA YARA A ZARIA

Miyagun iri da ke addabar masarautar Zazzau sun bude wuta inda su ka ji wa wani soja raunuka da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sa daga bisani.

Akasin ya auku a Milgoma da ke Daura da asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika.

Kazalika miyagun sun sace wata mata da ‘ya’yan ta.

Labarin ya nuna miyagun su kimanin 30 da makamai sun bude wuta yayin da jami’an su ka garzayo wajen don kawo dauki amma su ka samu hanyar tafiya da matar da kuma ji wa sojan rauni.

A kwanakin baya Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Bamalli ya koka cewa barayi sun addabi masarautar sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *