• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MIYAGUN IRI SUN TAKURAWA MASARAUTA TA-SARKIN ZAZZAU

ByYusuf Yau

Jun 15, 2021 , , ,

Sarkin Zazzau a jihar Kaduna Alhaji Ahmad Bamalli ya ce miyagun iri sun takurawa masarautar sa da kawo barazana ga lamuran tsaro.

Alhaji Bamalli na magana ne a fadar sa da ke Zaria yayin da tawagar lamuran tsaro daga Kaduna ta kawo ma sa ziyarar jaje.

Sarkin na magana ne kan yanda masu satar mutane da sauran ‘yan bimdiga su ka addabi yankin masarautar Zazzau.

A baya, matafiya kan shiga kwanciyar hankali in sun shigo yankin masarautar Zazzau musamman daga Kaduna amma yanzu ba haka lamarin ya ke ba, don har a yankin Jaji a kan samu miyagun iri na fakon jama’a.

Lamuran tsaro sun yi matukar tabarbarewa a yankin jihar Kaduna da kewaye.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *