Miyagun iri sun kai farmaki kan motar ‘yan sanda da ke sintiri a kamaran hukumar Ukwuani da ke jihar Delta.
Masu ta’addancin sun bude wuta a wata madakatar motoci inda su ka harbe ‘yan sandan uku da kuma cinna mu su wuta a motar su kirar sienna.
An baiyana cewa miyagun sun kona ‘yan ta’addan ta yanda ba ma za a iya gane su ba.
Jami’in labarun ‘yan sanda a jihar DSP Bright Edafe ya tabbatar da aukuwar mugun aikin amma bai samar da karin bayani ba.
Duk wannan yanayin tabarbarewar tsaro ne a dukkan sassan Najeriya.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀