• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MIYAGUN IRI SUN KASHE SHANU DA GAINAKO A LOBANTA JIHAR ABIA

ByNoblen

Jul 24, 2022

Miyagun iri sun yi kisan gilla ga mai kula da shanu da shanun masu yawa a Lobanta da ke jihar Abia.
Akwai babbar kasuwar shanu a garin na Lobanta da fataken shanu daga arewacin Najeriya ke kai shanu don sayarwa.
An samu gawar mai kula da shanun an kashe da datse kan sa baya ga yanke al’aurar sa.
Shugaban kungiyar fataken shanu Baba Sulaiaman Maikeke ya aza alhakin harin kan ‘yan awaren Biyafara na IPOB.
Maikeke ya kara da cewa an sha samun irin wannan akasi da ke nuna karin kiyaiya kan ‘yan arewa da ke zuwa fatauci yankin na kudu maso yammacin Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MIYAGUN IRI SUN KASHE SHANU DA GAINAKO A LOBANTA JIHAR ABIA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.