• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MIYAGUN IRI SUN BANKAWA OFISHIN HUKUMAR ZABE WUTA A JIHAR ENUGU

ByNoblen

Jul 6, 2022

Miyagun iri sun cinnawa ofishin hukumar zabe a Enugu wuta inda hakan ya kawo asarar kayan aiki a ofishin da harin ya shafa.

Hukumar zaben ta Najeriya INEC ta baiyana cewa harin ya faru ne kan ofishin hukumar da ke karamar hukumae Igbo-Eze ta arewa da ke jihar ta Enugu.

Duk da kokarin da hukumar kashe gobara ta yi na kashe wutar, amma an samu barna mai yawan gaske da ta hada da kujeru da akwatunan kada kuri’a.

INEC ta ce za ta duba ko harin ya shafi cigaba da rejistar samun katin zabe da a ke cigaba da gudanarwa.

Hare-hare kan cibiyoyin gwamnatin taraiya, jami’an tsaro da kuma musamman ‘yan arewa ya yawaita a wasu daga jihohin kudu maso gabashin Najeriya da ke da ‘yan awaren Biyafara na IPOB masu kashewa da lalata dukiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.