Ministan harkokin wajen Lebanon Charbel Wehbe ya yi murabus daga mukamin sa bayan caccaka mai zafi da ya samu daga kalaman da ya furta.
Wehbe dai ya dora alhakin karfin kungiyar ‘yan tawayen DAESH kan kasashen yankin tekun Pasha da hakan ya sanya ko ta wane bangare a ka yi ta Allah wadai da shi.
Wehbe ya yi kalaman ne a zantawa ta tashar talabijin ranar litinin.
Saudiyya ta mika wasikar watsi da kalaman na Wehbe ga jakadan Lebanon da kuma shi kan sa shugaban Lebanon Michel Aoun.
Wehbe ya ce ya na fata murabus din sa don amfanin al’ummar Lebanon ne kuma kalaman za su kwanta don cigaban hulda tsakanin Lebanon da kasashen larabawa.
Tuni ministar tsaron Lebanon Zeina Akar ta hau kujerar ministan waje na riko.
Hatta lauyoyi a Lebanon sun rubuta takardar korafin cewa Wehbe na neman tada wata fitina ce don haka a dau matakina kan sa.