• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MINISTAN SHARI’A MALAMI YA AIYANA TSAYAWA TAKARAR GWAMNAN JIHAR KEBBI A HUKUMANCE

Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya aiyana a hukumance zai yi takarar gwamnan jihar Kebbi a zaben 2023.
Malami ya baiyana wannan muradi a wani taron ‘yan jam’iyya a masaukin shugaban kasa a babban birnin jihar Kebbi wato Birnin Kebbi.
Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ke jagorantar taron inda shi da magoya bayan sa ke nuna mara baya ga muradin na Malami.
Ministan shari’ar wanda har yanzu bai ajiye mukamin sa ba don ba mamaki fakewa da wani hukuncin kotu, ya ce kasancewar sad an malamin addinin islama ba daidai ba ne ya nuna kwadayin shugabanci face mutane ne su ka ga cancantar sa.
Da alamu Malami ba shi da goyon bayan uban siyasar APC na Kebbi wato tsohon gwamnan jihar Sanata Adamu Aliero.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.