• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MINISTAN ABUJA MUHAMMAD MUSA BELLO YA KAMU DA CUTAR KORONA

Ministan babban birnin Najeriya Abuja Muhammadu Musa Bello ya kamu da cutar nan ta annoba korona bairos.
Sakataren na ofishin ministan Anthony Ogunleye ne ya baiyana labarin a wata sanarwar da a ka rabawa manema labaru.
Ministan dai a halin yanzu ya na gida don kula da lafiyar sa ta hanyar kebance kai kuma ya na yanayi mai kyawu don dama ya yi alluran rigakafi biyu.
Sanadiyyar kamuwa da wata mura da bushewar makogoro ya sa ministan zuwa don gwada lafiyar sa inda a ka samu ya kamu da korona.
Har yanzu a na shan mamakin yanda korona kan kama mutane masu samun kariyar gaske daga kamuwa da cutar.
Kwanan nan ma mai taimakawa shugaba Buhari kan labaru Garba Shehu ya ba da labarin warkewa daga cutar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *