• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MIKATI YA BUKACI ‘YAN LEBANON SU HADA KAI DON CETO KASAR SU

ByNoblen

Jun 25, 2022

Firaministan Lebanon Najib Mikati ya bukaci ‘yan kasar su hada kai don ceto kasar ta su daga halin durkushewar tattalin arziki da kasar ke fama da shi.

Mikati dai ya shigo aikin firaminista a mawuyacin yanayi da kasar ta taba a dukkan tarihin ta.

Yanayin siyasar kasar mai rabe-raben mukamai tsakanin ‘yan ahlusunnah, kirista da ‘yan shi’a na kaw tsaiko wajen samun hadin kai a dauki mataki na bai daya.

Mikati wanda biloniya ne ya na matsayin firaministan riko bayan kaddamar da shi da shugaba Michel Aoun ya yi da hakan ya nuna an samu tuntubar ‘yan majalisar dokokin kasar inda Mikati ya samu goyon bayan mutum 54 cikin 128.

Matukar Mikati ya gaza kafa gwamnati a wata hudu gabanin kammalar wa’adin Aoun a ranar 31 ga watan Oktoba, to ba wani tasiri ko amfani da za a samu a karkashin jagorancin sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MIKATI YA BUKACI ‘YAN LEBANON SU HADA KAI DON CETO KASAR SU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.