• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ME ZAI HANA MU RIKA NEMAN ZABIN ALLAH WAJEN NEMAN WADANDA ZA SU HAU MADAFUN IKO A NAJERIYA-TAMBAYAR MATASHI ALMUSTAHA HAJI SUFI

ByNoblen

Oct 3, 2020 ,

Matashi mai sharhi kan lamuran yau da kullum a arewa Al-Mustapha Haji Sufi ya jefa wata tambaya da ta kawo muhawara kan ko me ya sa jama’a kan na ce kan wani zabi tsakanin ‘yan takara na wanda ya ke burge su maimakon neman zabin Allah.

Almustapha Sufi daga Bauchi wanda almajiri ne, ya ce mutane kan nemi su gudanar da addu’a da ba su sunan wanda su ke so ya samu nasara a mukamin siyasa maimakon su ce a yi addu’a Allah ya zabawa jama’a mafi alheri. Sufi ya ce duk da Najeriya ba ta bin tsarin kowanne addini, amma don muhimmancin addini ya sa a kan rantsar da wanda ya lashe zabe da littafin da ya yarda da shi, da hakan ya nuna baiwa Allah zabi ga lamuran nasarar shugabanni shi zai kai Najeriya tudun mun tsira.

Yayin da ya ke nuna farin ciki ga alwashin shugaba Buhari na gadarwa Najeriya tsarin zabe mai inganci, Almustapha sufi ya shawarci masu zabe in Allah ya kai rai 2023 su mikawa Allah zabin nuna mu su mafi alheri.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ME ZAI HANA MU RIKA NEMAN ZABIN ALLAH WAJEN NEMAN WADANDA ZA SU HAU MADAFUN IKO A NAJERIYA-TAMBAYAR MATASHI ALMUSTAHA HAJI SUFI”
  1. Wonderful site you have here but I was curious about if you knew
    of any message boards that cover the same topics discussed here?

    I’d really love to be a part of community where I can get responses from other experienced
    individuals that share the same interest. If you have any suggestions, please let
    me know. Bless you!

Leave a Reply

Your email address will not be published.