• Fri. Jan 28th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ME YASA KA SHIRYA ZANGA-ZANGAR ADAWA DA SHUGABA BUHARI A LONDON OMOKRI?

Jagoran zanga-zangar adawa da zuwan shugaba Buhari London don karbar magani Reno Omokri ya ce babban dalilin shirya zanga-zangar don a bi kadun mutanen da ya ce an kashe ne a zanga-zangar endsars a Lekki da ke Lagos.

Omokri ya daidaici zuwan shugaba Buhari London, ya nufi kasar inda ya jagoranci zanga-zanga da bukatar shugaba Buhari ya dawo gida ya nemi magani.

Reno Omokri wanda tsohon mai taimakawa tsohon shugaba Jonathan ne, ya yi zargin an kashe makudan kudi wajen gyara asibitin fadar shugaban kasa, da kudin su ka kai a gyara asibiti da horar da likitocin da za su iya duba shugaban.

‘Yan sanda a London sun yi wa Omokri tambayoyi don hana shi wuce gona da iri a zanga-zangar ta adawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *