• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MATUKAR APC TA JUYAWA TINUBU BAYA ZA TA SHA KAYE WARWAS-ALHAJI MUHAMMADU MURTALA

Dan kwamitin kamfen din shugaba Buhari na BSO Alhaji Muhammadu Murtala ya nuna fargabar matukar APC ta juyawa uban jam’iyyar Bola Tinubu baya, za ta iya shan kaye a zaben 2023.

Muhammadu Murtala wanda ya shigo Abuja don halartar zaben na APC, ya ce yanda a ke shige da fice na neman wasu dabaru, ba za su taimaki jam’iyyar matukar ba gaskiya a ka gudanar a gaban kowa ba.

Yayin da ya ke cewa shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu bai dace ba da ya nuna zai ladabtar da Tinubu kan kalaman da ya yi na shi ne ya marawa Buhari baya ya lashe zabe a 2015, ya ce gaskiya gudunmwar da Tinubu ya bayar ba ta misaltuwa.

Dan siyasar ya ce ba lalle ne sai Tinubu ya zama shugaban Najeriya ba, amma ya na da hakkin a mutunta shi don sadaukar da kai da ya yi don ture mulkin PDP bayan shekaru 16.

Zuwa yanzu an daina batun rage yawan ‘yan takara a zaben na APC, inda alamu ke nuna jam’iyyar na sara ta na duba bakin gatari don gudun jifar kadangaren bakin tulu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.