• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MATSAYAR GWAMONIN KUDU NA MULKIN NAJERIYA KOMA KUDU NA JAWO MUHAWARA

Matsayar da gwamnonin kudancin Najeriya su ka fitar na shugabancin Najeriya a 2023 ya koma yankin su na jawo muhawarar muradin geamnonin da kai tsaye ya shafi jam’iyyar APC mai mulki ban da PDP mai adawa.

A zahiri alamu ma nun jam’iyyar da ke mulki ta fi tagomashin samun lashe zabe fiye da ta adawa da hakan kan sa hankali ya koma kan ta a lamuran mulkin karba-karba da ba ta cikin tsarin mulkin kasa.

Gwamonin wadanda kan hade kai su yi taro ba tare da bambancin jam’iyya ba, dun dau mataki a kwanakin baya na haramta kiwo da ‘yan arewa ne ke yi a dazukan yankin su.

Zuwa yanzu ba hakikanin bayani ko matsayar APC ga sashen da zai karbi tikitin jam’iyyar yayin da shugaba Buhari ke kammala wa’adi.

Manyan ‘yan jam’iyyar musamman daga arewa na nuna ya fi dacewa a biyewa cancantar dan takara fiye da yankin da ya fito.

Jam’iyyar PDP mai adawa ta yi nasarar gwada wanan tsari na karba-karba a 2007 inda bayan rasa nasarar tazarcen tsohon shugaba Obasanjo, ta kawo tikiti arewa inda marigayi shugaba ‘Yar’adu ya zama shugaba amma cikin ikon Allah mulkin ya koma kudu sanadiyyar rasuwar shugaban.

Wani dai dace a wancan lokacin shi ne kamfen din da ‘yan yankin kudu maso kudu ke yi cewa dan yankin su bai taba mulki ba, ya zo da ransar da Goodluck Jonathan wanda ya sake dawowa a 2011 ya kuma sake gwadawa a 2015 amma sai shugaba Buhari da ke cu daga arewa ya samu nasara.

Manyan sassan Najeriya sun hau karagar mulk wa imma a soja ko farar hula don haka yanzu ya rage a biyewa karba-karba ko cancanta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
9 thoughts on “MATSAYAR GWAMONIN KUDU NA MULKIN NAJERIYA KOMA KUDU NA JAWO MUHAWARA”
  1. Since the admin of this website is working, no doubt very quickly it will be well-known, due
    to its quality contents.

  2. Hello everyone, it’s my first go to see at this web site, and
    post is in fact fruitful designed for me, keep up posting such articles.

  3. I think the admin of this website is truly working hard in support of his web site, for
    the reason that here every information is quality based information.

Leave a Reply

Your email address will not be published.